IQNA

Karatun Kur'ani Tare Da Idris Hashemi Matashi Dan Kasar Afghanistan

Tehran (IQNA) karatun kur'ani tare da matashi mai suna Idris Hasemi dan kasar Afghanistan mazaunin kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Idris Hasemi dan kasar Afghanistan ne mazaunin birnin Jiddah na kasar Saudiyya tare da mahaifansa.

Tun kimanin shekaru 25 ad suka gabata ne Sayyid Amin hasemi mahaifin Idris Hashemi ya yi hijira tare da iyakansa zuwa birnin Jidda na kasar saudiyya, inda yake rayuwa a halin yanzu.

Idris ya hardace kur'ani mai tsarki, sanann kuma yana da hazaka matuka wajen karatun kur'ani da kuma addini, inda a shekara ta 2016 shi ne ya zo na daya gasar karatun kur'ani ta duniya a kasar Saudiyya.

A cikin wannan faifan bidiyon za a saurari karatun ayoyi na 30 zuwa 36 a cikin surat Fussilat tare da Idris.

 

3994895