IQNA

Taron Janazar Marigayi Sayyid Muhammad Sa'id Hakim A Yau A Birnin Najaf na Iraki

15:58 - September 05, 2021
Lambar Labari: 3486272
Tejran (IQNA) a yau ne aka gudanar da janazar babban malamin addinin muslunci Ayatollah Sayyid Muhammad said Hakim a birnin Najaf na Iraki

Tashar Alghadir ta bayar da rahoton cewa, a yau ne aka gudaar da janazar babban malamin addinin muslunci Ayatollah Sayyid Muhammad Sa'id Hakim a birnin Najaf na Iraki, bayan da Allah ya yi masa rasuwa a ranar Juma'a da ta gabata.

An bizne gawar marigayin a wata makabarta da ake bizne iyalan Hakim, wadanda suka hada da manyan malamai da aka yi a kasar Iraki, makabartar da take kusa da hubbaren Imam Ali (AS) a birnin Najaf.

Taron janazar ya samu halartar manyan malaman addini daga sassa na kasar Iraki, da kuma shugabannin kabilun larabawan kasar da kuma sauran kabilu, gami da jami'an gwamnatin kasar.

 
captcha