IQNA

An Dawo Da Karatun Halqa A Masallacin Ma’aiki (SAW)  A Madina

22:32 - September 05, 2021
Lambar Labari: 3486275
Tehran (IQNA) an dawo da karatun halqa da aka saba gudanarwa a masallacin ma’aiki (SAW)

Kamfanin dillancin labaran Al’ain ya bayar da rahoton cewa, kwamitin kula da masallacin manzon Allah (SAW) ya sanar da cewa, an dawo da karatun halqa da aka saba gudanarwa a masallacin mai alfarma.

A ranar laraba da ta gabata ce aka gudanar da lacca ta addini ta farko a masallacin manzo (SAW) tun bayan bullar cutar corona, inda aka dakatar da laccoci da sauran bayanai da aka saba yi an addini a cikin wannan masallaci, saboda dalilai na kiwon lafiya.

Sheikh Abdulrahman Al-sudais ne ya gabatar da laccar, wanda ya yi bayani kan muhimman abubuwan da suka rataya a kan musulmi su kiyaye musamman lokacin da aka samu bullar annoba irin wadda ta game duniya.

Tun daga lokacin da cutar ta bulla ne dai aka dakatar da karatun halqa da ake a cikin masallacin ma’aiki (SAW) wanda mutane suke yin karatun littafai a wajen malamai na fikihu da hadisi da kuma tafsiri da sauran bangarori na ilimi.

3995238

 

Abubuwan Da Ya Shafa: karatun halqa
captcha