IQNA

An Haramta Wa Dan Wasan Judon Aljeriya Yin Wasa Tsawon Shekaru 10 Sadoda Kin Wasa Da Bayahuden Isra'ila

16:21 - September 08, 2021
Lambar Labari: 3486284
Tehran (IQNA) an haramta wa dan wasan Judo na Aljeriya yin wasa har tsawon shekaru 10 saboda kin yin wasa da bayahuden Isra'ila.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, hukumar wasannin Judo ta duniya ta dauki matakin haramta wa dan wasan Judo na Aljeriya Fathi Nurain yin wasa har tsawon shekaru 10 saboda kin yin wasa da bayahuden Isra'ilaa  wasannin motsa jiki na Tokyo 2020.

Rahoton ya ce wannan mataki ya shafi har da mai horar da dan wasan na Aljeriya Ammar Bin Yakhluf, wanda ya goyi bayan dan wasan.

Dan wasan an Aljeriya ya ce ya dauki wannan matakin ne na kin yin wasa da bayahuden Isra'ila, saboda nuna adawarsa da zaluncin da Isra'ila take yi kan al'ummar Falastinu.

Ya ce bai yi nadama kan matakin da ya dauka ba, domin kuwa ya san cewa abin ya yi saboda Allah ne ya yi, domin nuna goyon bayansa ga gaskiya da kuma kare akidarsa.

 

Abubuwan Da Ya Shafa: dan wasan Aljeriya
captcha