IQNA

Taliban Ta Sanar Da Sunayen Ministocin Sabuwar Gwamnatin Da Ta Kafa

22:06 - September 08, 2021
Lambar Labari: 3486286
Tehran (IQNA) Kungiyar Taliban a Afghanistan ta sanar da kafa sabuwar gwamnati a wannan Talata.

Kakakin kungiyar ne Zabihullah Mujahid ya sanar da mambobin sabuwar gwamnatin da ministoci daban-daban, makonni uku bayan kwace mulki daga hannun gwamnatin Kabul.

Mullah Muhammad Hassan Akhund, daya daga cikin wandanda suka kafa kungiyar, an nada shi a mukamin Firaminista na Afghanistan.

An nada Mullah Abdul Ghani Baradar a matsayin Mataimakin fira minista.

Sauren mambobin sabuwar gwamnatin da aka sanar da nadin nasu, sun hada da Sarrajuddin Haqqani wanda zai zama ministan harkokin cikin gida, sai Mullah Yaqoob zai zama ministan tsaro, yayin da Abas Stanikzai kuma zai zama mukadashin ministan harkokin waje.

A nata bangaren gwamnatin Iran ta bayyana cewa, abin da kasar Afghanistan ke bukata a halin yanzu shi ne kwanciyar hankali da zaman lafiya.

A cikin wani bayani da ya saka a shafinsa na twitter a yau Alhamis, shugaban majalisar koli ta tsaron kasa a Iran Admiral Ali Shamkhani ya bayyana cewa, abin da kasar Afghanistan ke bukata a halin yanzu shi ne kwanciyar hankali da zaman lafiya, tare da rashin tsoma baki na kasashen ketare a cikin harkokin kasar.

Ya ce al’ummar Afghanistan sun sha wahalhalu sakamakon shigar shugula da kasashen duniya suka yi a  cikin harkokin kasarsu, wanda hakan ne babban abin da ya jefa kasar cikin mawuyacin hali tsawon shekarun da tayi kasashen yammaci na mamaye da ita.

Ya ce, Iran tana goyon bayan fifita hanyoyi na samun sulhu da fahimtar juna tsakanin al’ummar kasar Afghanistan, wanda hakan ba zai samu ba sai ta hanyar samun fahimtar juna tsakanin dukkanin bangarori na al’ummar kasar.

Daga karshe ya jaddada kira kan wajabcin hada karfi da karfe tsakanin dukkanin bangarori na al’ummar kasar tare da yin aiki tare domin ci gaban kasarsu, ba tare da mayar da wani bangare saniyar ware ba.

 

Abubuwan Da Ya Shafa: sulhu kwanciyar hankali zaman lafiya
captcha