IQNA

Sheikh Ibrahim Alwazin: Rashin Sahihiyar Fahimtar Ayoyin Kur'ani Ne Ke Kai Wasu Shiga Ayyukan Ta'adanci

18:00 - September 09, 2021
Lambar Labari: 3486289
Tehran (IQNA) Sheikh Ibrahim Alwazin daya ne daga cikin malaman cibiyar ilimi ta Azhar, wanda ya bayyana cewa, rashin sahihiyar fahimta kan ayoyin kur'ani ne ke wasu shiga ayyukan ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a wani zaman karawa juna sani na daliban jami'a da da sheikh Ibrahim Wazin daya daga cikin malaman cibiyar ilimi ta Azhar ya shiya, ya bayyana cewa, rashin sahihiyar fahimta kan ayoyin kur'ani ne ke wasu shiga ayyukan ta'addanci da sunan addini.

Malamin ya kirayi zaman taron ne a bangaren koyar da ilimin kur'ani na jami'ar Diqhaliyya a kasar Masar, da nufin yin bayani na fadakawrwa ga daliban ilimi.

A cikin bayanin nasa ya yi ishara da yadda wasu daga cikin masu karkatacciyar fahimta kan kur'ani da sunnar manzo (SAW) da ma adinin kansa suke yin amfani da karkatacciyar fahimtarsu kan ayoyin kur'ani da sunnar ma'aiki wajen saka matasa cikin ayyukan ta'addanci da sunan jihadi.

Ya ce wannana bu ne da ya kamata a gyara shi ta hanyar fadakarwa, kuma nauyi ne a matakin farko da ya rataya kan malaman addini da hukumomi na kasashen musulmi.

kasar Masar dai a halin yanzu tana daga cikin kasashen larabawa da ake samun karuwar masu tsatsauran ra'ayi na Salafiyya, wadanda galibi su ne suke shiga kungiyoyin da ake kira na jihadi da suke kaddamar da ayyukan ta'addanci da sunan jihadi.

تأکید استاد مصری بر فهم صحیح قرآن برای مقابله با ادعاهای تروریست‌ها

تأکید استاد مصری بر فهم صحیح قرآن برای مقابله با ادعاهای تروریست‌ها

 

3996320

 

captcha