IQNA

Za A Gudanar Da Taron Gidajen Radiyo Na Kasashen Musulmi

17:34 - September 13, 2021
Lambar Labari: 3486303
Tehran (IQNA) shugaban cibiyar kula da harkokin gidajen radiyo na kasashen musulmi ya gana da babban malamin Azhar.

Shafin jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, a jiya shugaban cibiyar kula da harkokin gidajen radiyo na kasashen musulmi Amru Laisi ya gana da babban malamin Azhar Sheikh Ahmad Tayyib a ofishinsa da ke birnin Alkahira.

A yayin wannan ganawa bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da suka shafi ayyukan kafofin yada labarai na kasashen musulmi da kuma ayyukan da suke gudanarwa na wayar da kan al'umma.

Babban malamin na Azhar da kuma shugaban cibiyar kula da harkokin gidajen radiyo na kasashen musulmi sun cimma matsaya kan gudanar da taro na kasa da kasa na gidajen rediyon kasashen kasashen musulmi, musamamn na kur'ani.

Babbar manufar taron dai ita ce kara fayyace muhimman ayyuka da suka shafi sadarwa a kasashen musulmi, inda masana za su gabar da bayanai kan hakan

Baya ga haka kuma sun cimma matsaya kan bayar da horo na musamman dangane da ayyukan kafofin yada labarai an musulmi, wanda cibiyar Azhar za ta dauki nauyinsa.

An kafa cibiyar kula da harkokin gidajen radiyo na kasashen musulmi zaman taron karo na 6 na kungiyar kasashen musulmi ta OIC a shekara ta 1975, kuma wannan cibiya tana karkashin kungiyar kasashen musulmi ne.

3997112

 

 

captcha