IQNA

Jami’ar Sudan Ta Nuna Wani Sabon Furoje Na Kammala Digiri Na Uku A Ilimin Addini

22:58 - September 20, 2021
Lambar Labari: 3486332
Tehran (IQNA) babbar jami’ar Sudan ta nuna wani sabon rubutu da wani mai bincike ya yi kan ilimin kur’ani.

Shafin tahdith net ya bayar da rahoton cewa, babbar jami’ar Sudan ta nuna wani sabon rubutu da wani mai bincike ya yi kan ilimin kur’ani, wanda shi ne irinsa na farko a bisa wannan salo.

Ramzi Hamidi shi ne wanda ya rubuta wannan risala ta Furoje a kan ilmomin kur'ani mai tsarki, inda ya yi bayani ta hanyar salo na musamman dangane da ilmomin da suke cikin kur'ani a zamanance.

Kasantuwar Ramzi mutum ne mai bincike a kan ilmomi daban-daban, hakan ya taimaka masa matuka wajen gano abubuwa da dama da kur'ani yake magana a kansu dangane da halittu da kuma sararin samaniya, da tekuna da tsirrai da halittu.

Kasantuwar wanann shi ne karon farko da aka rubuta irin wannan furoje na binciken ilmomi a cikin kur'ani a jami'ar Sudan, wannan sanya an ba shi muhimmanci matuka fiye da dukkanin sauran ayyukan bincike da aka gudanar a jami'ar.

 

 

 

3998579

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: sabon rubutu ، wannan salo ، bincike ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha