IQNA

Jerin Gwanon Goyon Bayan Al'ummar Falastinu A Kasar Argentina

23:12 - September 24, 2021
Lambar Labari: 3486346
Tehran (IQNA) al'ummar kasar Argentina sun gudanar da jerin gwanon nuna goyon baya ga al'ummar Falastinu.

Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa, al'ummar birnin Beonos Aires na kasar Argentina sun gudanar da jerin gwanon nuna goyon baya ga al'ummar Falastinu.

Masu jerin gwanon sun daga tutocin Falastnu, tare da rera taken nuna cikakken goyon bayansu ga gwagwarmayar Falastinawa da suke yi, sakamakon mamayar yankunansu da Isra'ila take yi.

Haka nan kuma masu zanga-zangar sun nuna goyon bayansu ga Falastinawa 6 da suka kubutar da kansu daga gidan kason Isra'ila a kwanakin baya, wadanda daga bisani Isra'ila ta sake kama su.

A halin yanzu dai akwai Falastinawa 4850 da suke tsare a gidajen kason Isra'ila guda 23, daga cikinsu kuma har da mata 41, da kananan yara 225.

 

3999757

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: birnin Beonos Aires ، kasar Argentina ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha