Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, masu fafutukar kafafen sada zumunta sun jaddada muhimmancin daukar matakin gaggawa a kan mabiya addinin Hindu da kuma hana munanan ayyukansu a kan musulmi.
Haka nan kuma sun yi Allah wadai da wulakanta wuraren ibadar musulmi da mabiya addinin Hindu suke yi, tare da wallafa hotuna da bidiyo na irin wadannan wurare a shafukan yanar gizo domin duniya ta gani.
Daya daga cikin waɗannan bidiyon yana nuna wani wuri da aka lalata masallatai da matasan Hindu suka yi.
Wasu bidiyo sun nuna yadda ake azabtar da Musulmai da barazanar kisan a kansu, kuma wasu matasan Hindu suna amfani da takubba don yi wa Musulman Kashmir kisan kare dangi.
Bidiyoyin da dama da aka saki a yanar gizo a 'yan kwanakin da suka gabata sun kuma nuna 'yan Hindu suna kai hari kan masallatai da kona kwafin Alkur'ani, suna yin ƙazanta a wuraren ibadar Musulmi.