IQNA

Limamin Masallacin Aqsa: Kotun Isra'ila Ba Ta Da Hurumin Halastawa Yahudawa Keta Alfarmar Masallacin Aqsa

19:50 - October 08, 2021
Lambar Labari: 3486401
Tehran (IQNA) Limamin masallacin Aqsa ya mayar da martani kan hukuncin kotun Isra'ila da ya halastawa yahudawa yin ayyukansu na ibada a cikin wannan masallaci.

Tashar russia Today ta bayar da rahoton cewa, Sheikh Ikramah Sabri Limamin Juma'a a masallacin Aqsa ya mayar da martani kan hukuncin kotun Isra'ila da ya halastawa yahudawa yin ayyukansu na ibada a cikin wannan masallaci, inda ya ce kotun Isra'ila ba ta da wannan hurumi.

Ya ci gaba da cewa, wannan hukunci na kotun Isra'ila da ya bai wa yahudawa damar yin abin da suka ga dama cikin masallacin Quds da sunan ibada ko raya wasu abubuwa na addini, yin hakan shi kansa wani nau'in shisshigi ne a kan wannan masallaci.

Kuma a cewarsa, wannan wani shiri ne daga shirye-shiryen da yahudawan suke da shi na kwace iko da wannan masallaci, tare da mayar da shi wurin harkokinsu, da kuma haramta wa musulmi yin ibada a cikinsa, wanda kuma a cewar malamin ba za su amince da hakan ba matukar dai suan a raye.

 

4003095

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: shirye-shiryen masallacin aqsa matukar
captcha