Rahotanni daga Iraki sun ce a yau dubban mutane nevsuka taru a hubbaren Imam Hassan Al-askari (AS) da ke birnin Samirra a kasar Iraki, domin tunawa da zagayowar lokacin shahadarsa.
A kowace shekara masoya ahlul bait daga sassa na kasar Iraki da ma wasu kasashen ketare suna taruwa a wannan hubbare na Imam Hassan Al-askari (AS) jikan manzon Allah (SAW) domin tunawa da lzagayowar okacin haihuwarsa ko shahadarsa.