IQNA

Sudan Na Adawa Da Bayar Da Kujera Ga Gwamnatin Isra'ila A Tarayyar Afirka

20:02 - October 15, 2021
Lambar Labari: 3486430
Tehran (IQNA) Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta fitar ta ce tana adawa da nadin Isra'ila a matsayin mamba mai sanya ido a kungiyar Tarayyar Afirka.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta fitar ta ce tana adawa da baiwa Isra'ila kujera a kungiyar Tarayyar Afirka a matsayin mamba mai sanya ido a kungiyar.

Bayanin ya ce, muna adawa da shawarar da babban Kwamishinan Tarayyar Afirka ya bayar na bai wa Isra’ila kujear mamba na masu sa ido kafin yin shawarwari da tuntubar kasashe mambobin kungiyar, kuma wannan ya haifar da sabani tsakanin Kwamishinan da mambobin.

Sanarwar ta ce "wannan tsarin kuma ya sabawa ka'idojin kungiyar Tarayyar Afirka, wacce ke jaddada ruhin hadin kai, mutunta juna da kuma cimma matsaya."
 
Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta kara da cewa: Ministar harkokin wajen kasar Maryam Sadegh Mehdi ba za ta halarci taron wa'adin na 9 na majalisar zartarwar kungiyar Tarayyar Afirka ba saboda ayyukan cikin gida da kuma wasu ayyukan masu alaka da wasu muhimman batutuwa na kasa, inda mataimakinta  Mohammad Sharif Abdullah ne zai ta halarci taron a madadinta.
 
A watan Agusta, babban Kwamishinan Tarayyar Afirka Musa Faki, ya amince Isra'ila ta zama mamba mai sanya ido a kungiyar.
 
Biyo bayan shawarar da ofishin shugaban kungiyar tarayyar Afirka ta yanke, Aljeriya da wasu kasashen Larabawa bakwai sun yi nuna kin amincewarsu da wannan mataki.
 
A kwanakin baya ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta sanar a cikin wata sanarwa cewa jakadanta a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha ya mika takardunsa ga kungiyar Tarayyar Afirka a matsayin mamba mai sanya ido.
 
Gwamnatin Sahayoniya ta taba yin aiki a matsayin mai sa ido a kungiyar Hadin Kan Afirka, amma bayan rushewarta a 2002 da kuma canzawa zuwa Tarayyar Afirka, kokarin da gwamnatin ta yi na ci gaba da zama mamba a matsayin mai sa ido bai ci nasara ba.
 
 

4005093

 

 
 
 
 
Abubuwan Da Ya Shafa: babban Kwamishina tarayyar Afirka
captcha