IQNA

Taron Makon Hadin Kan Musulmi: Manzon Allah (SAW) Shi Ne Malamin Kur'ani Na Farko

16:50 - October 21, 2021
Lambar Labari: 3486454
Tehran (IQNA) mahalarta taron makon hadin kai sun bayyana manzon Allah (SAW) a matsayin babban malamin kur'ani na farko.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a babban taron makon hadin kan al'ummar musulmi da ake gudanarwa yanzu haka a birnin Tehran, wanda masana da malamai daga sassa daban-daban na duniya suke halarta kai tsaye a dakin taron, yayin da kuma wasu suke halarta ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo, mahalarta taron sun ce manzon Allah shi ne malamin kur'ani na farko.

Haka nan kuma sun tabo batutuwa daban-daban da suka shafi duniyar musulmi, wanda matukar dai ana son yin koyi da manzo, akwai abubuwa da dama da ya kamata gwamnatocin kasashen musulmi su kiayye su a  matsayi na siyasar cikin gida da kuma siyasar kasa da kasa, kamar batun karkata ga yahudawa da wasu kasashen msuulmi suke yia  yanzu tare da kulla alaka da Sahyuniyawa, duk da irin cin zalun da suke yi wa al'ummar falastinu, da kuam tozarta wurare masu tsarki na musulmi a Quds da sauransu.

Daya daga cikin manyan malamai daga Iraki Sayyid Ahmad Al'araji ya yi tambaya cewa: Shin daidaiton alakar da ke tsakanin shugabannin wasu ƙasashen larabawa da Isra’ila ta ginu ne a kan daidaito da junansu? Ya ce: Ya kamata a ce babu wani sabani da shubuha a cikin alakar da ke tsakanin masu daidaita alaka da mahukuntan larabawa irin su hadaddiyar daular larabawa da Bahrain wadanda suke son a daidaita alakarsu da gwamnatin yahudawa.

 

 

4006677

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha