A cikin wannan faifan bidiyo da ke kasa, za a iya sauaren tilawar kur'ani mai tsarki tare da fitaccen makaranci dan kasar Iraki Muhammad Ridha Al-zubaidi, wanda ya karanta aya ta 13 a cikin surat Hujrat.
Wannan aya mai albarka tana yin bayani ne kan yadda kur'ani mai tsarki yake sanya ma'auni na fifiko a tsakanin dukkanin bil adama, ta yadda ya banbance cewa, fifiko a tsakanin 'yan adam ba shi da alaka da launin fata ko kabila, ma'anin samun matsayi da fifiko a wurin Allah shi ne jin tsoransa, wato taqwa.