IQNA

An Ci Gaba Da Yin Allawadai da Juyin Mulki A Kasar Sudan

16:07 - October 26, 2021
Lambar Labari: 3486477
Tehran (IQNA) ana ci gaba da yin tir da Allawadai da juyin mulkin da sojoji suka yia kasar Sudan.

Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na ci gaba da yin allawadai da juyin mulki a Sudan.

Babban sakatare janar na MDD, Antonio Guterres, ya yi, tir da abunda ya danganta da juyin mulkin soji dake faruwa a Sudan, tare da kiran a gaggauta sakin dukkan manyan ‘yan siyasa da ake tsare da ba tare da wata wata ba.
 
Kungiyar tarayyar Afrika ma ta fitar da irin wanan sanarwa inda ta bukaci sojoji da farar hula a kasar dasu koma tattaunawa a tsakaninsu domin ceto kasar daga halin da ta tsunduma.
 
Kungiyar kasashen Larabawa ita ma ta bukaci dukkan bangarorin dasu mutunta yarjejeniyar raba mulkin rikon kwarya da suka cimma a 2019, bayan kifar da mulkin Umar Al-bashir.
 
Kwamitin kungiyar tarayyar turai kuwa ya bukaci da kaucewa zubar da jinni.
 
Shugaban faransa Emanuel Macron, ya bukaci a mutunta hurimin firaministan na Sudan da kuma na magabata ‘yan siyasa.
 
Amurka dai ta ce ta dakatar da tallafin jin kai da take baiwa kasar ta Sudan.
 
A wani lokaci nan gaba ne ake sa ran kwamitin tsaron MDD, zai yi zama kan hali da ake ciki a kasar ta Sudan, bayan da juyin mulkin da sojoji sukayi tare da kame mambobin gwamnatin rikon kwarya ciki har da firaminista Abdallah Hamdok.
 

4007877

 

captcha