IQNA

Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Adawa Da Juyin Mulki A Kasar Sudan

15:42 - October 31, 2021
Lambar Labari: 3486494
Tehran (IQNA) ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa da juyin mulkin sojoji a kasar Sudan.

Dubban masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin sojoji a kasar Sudan ne suka fantsama kan tituna tun daga jiya Asabar, domin nuna goyon bayansu ga tsarin mulkin dimokradiyya a kasar.

Zanga-zangar ta zo ne kusan mako guda bayan da sojoji suka tsare shugabannin farar hula na Sudan a ranar Litinin da ta gabata, tare da rusa gwamnatin rikon kwaryar dake jagoranci da kuma ayyana dokar ta baci, lamarin da ya janyo wa sojojin Allawadai daga kasashen duniya.

Kawo yanzu akalla mutane sha biyu suka mutu, yayin da wasu kusan 200 suka jikkata sakamakon arangama tsakanin masu jerin gwano da kuma jami’an soji tun bayan soma zanga-zangar adawa da juyin mulkin na Sudan.

Duk da zubar da jinin da ake samu, amma masu shirya zanga-zangar suka sha alwashin jagorantar sake fitar mutane akalla miliyan 1, don nuna adawa da kwace madafun iko da sojoji ke yi, kwatankwacin zanga-zangar da ta kai ga hambarar da gwamnatin tsohon shugaba Omar al-Bashir a shekarar 2019.

Dubban mutane ne suka taru a Khartoum, babban birnin Sudan da kuma garuruwan Omdurman da Khartoum ta Arewa.

 

4009229

 

captcha