IQNA

Gwamnatin Saudiyya: Babbar Matsalarmu A Lebanon Ita Ce Hizbullah

16:00 - November 01, 2021
Lambar Labari: 3486498
Tehran (IQNA) ministan harkokin wajen Saudiyya ya ce, kungiyar Hizbullah ita ce babbar matsalarsu, da kuma babban dasirin da take da shi a kasar Lebanon.

Faisal bin Farhan ya bayyana hakan ne a zantawarsa da tashar talabijin ta CNBC ne a jiya Lahadi, dangane da halin da ake ciki a dangantakar Saudiyya da Lebanon biyo bayan sake yada wasu tsoffin kalamai  da ministan yada labaran Lebanon George Qardahi ya yi, na yin Allah wadai da harin da Saudiyya da kawayenta suke kaddamarwa kan al’ummar kasar Yamen.

A dai dai lokacin mahukuntan masarautar  ya’yan gidan Al Saud suke kara tsananta kalamansu na batunci a kan Hizbullah, da kuma neman haifar da rikici a cikin kasar ta Lebanon, a nasu bangaren jagororin kungiyar ta Hizbullah na kokarin ganin cewa an kauce wa duk wani abin da zai iya kawo rudani da rikcin cikin gida a kasar ta Lebanon sakamakon matakan da gwamnatin Saudiyya take dauka domin ganin hakan ta faru.

A wani bangare na jawabin babban sakataren kungiyar Hizbullah da ya yi a kwanakin baya, Sayyid Hasan Nasrallah ya yi ishara da cewa, a yau a kasar Labanon "Hizbullah" ita ce ta farko da ake kai wa hari, kuma ana neman ganin an haifar da yakin basasa a kasar a kasar Lebanon, amma Hizbullah ba za ta taba bari masu wannan manufa su cimma burinsu ba.

Da dama daga cikin bangarorin siyasa da kungiyoyi a kasar at Lebanon sun nuan cikakken goyon bayansu ga Qardahi, tare da yin tir da Allawadai da matsin lambar masarautar Al saud a kan Lebanon, inda suke kiran wannan masarauta idan har tana jin jarunta ne, to ba a kan Lebanon za ta nuna jarunta ba, ya kamata a ji martaninta ne  a lokacin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa sarki Salman wulakanci da cin zarafi da tozarta shi a idon duniya, wanda kuma har yanzu  masarautar Al Saud ba ta iya mayar da martani kan hakan ba, ko da kuwa ta hanyar yin Allawadai ne da hakan.

4009664

 

 

captcha