Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, Tawagar jami'an hukumar leken asirin haramtacciyar kasar Isra'ila (Mossad) ta gana da wani jami'in sojin Sudan a birnin Khartoum a makon jiya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Sudan.
Jaridar Yedioth Ahronoth ta yahudawa ta rawaito cewa makasudin ziyarar tawagar Isra'ila a Sudan ba shi ne neman sasanta bangarorin da ke rikici a kasar ba, Isra'ila ta aike da tawaga ne domin fahimtar halin da ake ciki a Sudan.
A cewar jaridar, bayan rugujewar gwamnatin Sudan da majalisar gudanarwar kasar, Tel Aviv wadda ta yi kokarin daidaita hulda da Khartoum a yarjejeniyar Abraham da Amurka ta shirya, tana neman sanin gaskiyar halin da ake ciki a Sudan.
A cewar wani jami'in diflomasiyyar kasashen yammacin duniya, Mohammad Hamdan Daqlu kwamandan rundunar sojojin kasar Sudan, ya gana da tawagar yahudawan na Isra'ila da suka ziyarci kasar ta Sudan.