
Shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, Azhar ta bayyana matakin da wata makaranta a kasar Spain ta dauka na haramta wa wata daliba musulma sanya hijabi a makaranta da cewa, baya ga kasantuwar hakan nuna wariya ne, haka nan kuma yana da hadari a cikin zamantakewar al'umma da hadin kanta.
Al-Azhar ta tabbatar da cewa tana bibiyar sakamakon matakin da makarantar kasar Spain ta dauka, tana mai cewa: Irin wadannan matakai suna da hadari ga zaman tare da hadin kan al'umma, domin wannan hukunci wani nau'i ne na nuna wariya ga musulmi a makarantu.
bayanin ya kara da cewa: A cewar jaridar Periodico CLM ta kasar Spain, 'yan kasar da dama ne suka yi gangami a kusa da makarantar domin nuna goyon bayansu ga wannan daliba musulma, suna daga tutoci da kuma rera taken rashin amincewa da nuna kyama ga musulmi.
Suna rera taken cewa "hijabi yana rufe gashi ne ba hankali ba"; Amma amma duk da hakan wannan bai sanya makarantar ta janye matakin da ta dauka ba.
Mahaifiyar dalibar ta nuna rashin gamsuwarta da matakin da makarantar ta dauka, inda ta ce diyarta na sha’awar sanya hijabi kuma rashin saka hijabin zai yi mummunan tasiri a cikin ranta.