IQNA

Taron Kara Wa Juna Sani Mai Taken "Magabatan Quds" A Mauritaniya

20:48 - November 08, 2021
Lambar Labari: 3486529
Tehran (IQNA) An fara taron karawa juna sani na "Majagaban Kudus" karo na hudu a Nouakchott babban birnin kasar Mauritania.

Shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, Taron wanda aka gudanar domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu, ya samu halartar tawaga daga kungiyar Hamas da wakilai daga wasu kasashen Afirka, da kuma wasu malamai da 'yan siyasa da 'yan majalisar dokokin Mauritaniya.


Kungiyar agaji da kuma kare al'amuran adalci na al'ummar Falastinu, wadda kungiya ce mai zaman kanta a kasar Mauritania, tare da hadin gwiwar kungiyar hadin kan kasa da kasa don tallafawa al'ummar Palastinu ne suka shirya taron na Al-Quds Pioneers Seminar.

Taron wanda aka fara a jiya da taken "Majagaba na Kudus suna rike da takobi" wanda kuma ake ci gaba da yi na tsawon kwanaki biyu, ana gudanar da bita kan al'amuran Palastinu da dabarun tallafawa al'ummar Palasdinu a Mauritaniya da yammacin Afirka.

Shi ma Sami Abu Zuhri daya daga cikin kusoshin kungiyar Hamas, ya jaddada a cikin jawabinsa a wajen taron cewa, duk da matsalolin da suke fuskanta, an sun samu damar kera makamai da kuma shirin tunkarar makiya a yankin zirin Gaza.

Ya kuma yaba da matakin da Mauritaniya ta dauka kan goyon bayanta ga al'ummar Falastinu, da kuma tsayin dakan da ta yi kan hakan, duk kuwa da matsin lambar da ake yi a kanta na kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra'ila, amma Mauritaniya taki yin hakan, saboda tabbatar wa duniya cewa ba ta yarda da zaluncin gwamnatin yahudawan Isra'ila a kan al'ummar Falastinu ba.

 

4011252

 

captcha