IQNA

Abdulazim Al-Hassani Daya Daga Cikin Manyan Malaman Ahlul Bait

14:23 - November 10, 2021
Lambar Labari: 3486537
Tehran (IQNA) Sayyid Abdulazim Hasani na daga cikin manyan malaman ahlul bait (AS) da suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen ilamntar da al'ummar Manzon Allah (SAW)

Shekaru 1270 da suka gabata a ranar hudu ga watan Rabiu Sani shekara ta 173 hq, aka haifi Abdulazim a birnin Madina mai alfarma, wanda kuma shi daya ne daga cikin jikokin Imam Hassan Mujtaba (AS).

Ya kasance daya daga cikin na hannun damar Imam Aliyu Hadi (AS) kuma ya nakalto ruwayoyi masu tarin yawa daga Imam hadi (AS) baya ga haka kuma ya nakalto ruwayoyi daga wasu limaman Ahlul bait, musamman Imam Ridha(AS) da kuma Imam Muhamamd Jawad (AS).

Daga bisani Imam Hadi (AS) ya umarce shi da ya tafi Iran domin ilmantar da mutane da kuma nuna musu sahihin tafarki na addinin musulunci bisa koyarwar manzon Allah (SAW) da kuma Ahlul bait (AS).

Abdulazim ya tafi Iran, inda ya yada zango a birnin Ray wanda yake kusa da birnin Tehran a yanzu, inda a nan ya yi rayuwarsa, ya yada ilimin addinin musulunci bisa koyarwar manzon Allah da ahlul bait a kasar Iran.

Ya kasance malami mai tsoron Allah da gudun duniya da kuma sadaukarwa a kan tafarkin addini.

Daga karshe a cikin watan Shawwal hijira ta 250 ya rasu, kuma har yanzu hubbarensa na nan garin rai, a kullum rana dubban musulmi masoya ahlul bait (AS) a ciki da wajen kasar Iran suna ziyartarsa.

4012051

 

 

captcha