Shafin CNET ya bayar da rahoton cewa, bayan da aka wallafa hotunan cin mutuncin kur’ani mai tsarki a shafin Twitter a ranar Larabar da ta gabata, wanda mutane da dama suka bukaci a cire shi, kamfanin Activision wanda ya shirya wasan ya bayyana cewa zai gyara matsalar tare da ba da hakuri.
Mai magana da yawun kamfanin na Activision ya fada a cikin wata sanarwa cewa: “An yi kiran yin aikin ne ga kowa da kowa. Akwai bayanai masu mahimmanci ga al'ummar musulmi da aka yi kuskure a cikin wasan kuma yanzu an cire su daga wasan.
Kmafanin ya ce bai kamata hakan ya bayyana a cikin wasan ba, Muna ba da hakuri sosai kuma muna ƙoƙari kada mu bar irin waɗannan abubuwa su faru a nan gaba.
A wani bangare na taswirar Call of Duty Vanguard da ke sashen aljanu, an rika nuna wasu shafukan kur'ani mai tsarki.