IQNA

Bikin Fasahar Musulunci A Birnin Houston na Amurka

22:22 - November 14, 2021
Lambar Labari: 3486558
Tehran (IQNA) Za a gudanar da bikin ayyukan fasahar Islama karo na 8 a birnin Houston na jihar Texas ta kasar Amurka.
Ana gudanar da bikin ne tare da halartar mutane a cikin Masallacin Al-Salam da ke yankin bazara na birnin Houston a jihar Texas, kuma ana saka shi akan layi na yanar gizo.
 
Za a yi wannan biki ne a ranar Lahadi 12 ga Disamba na karshen wannan shekara da muke ciki.
 
Bikin ya ƙunshi ayyukan masu fasaha daga ko'ina cikin Amurka. Masu ziyara za su iya samun damar siyan kyawawan ayyukan fasaha akan layi da kuma duba su a wurin bikin.
 
Rahoton ya ce, a gefen bikin, za a nuna wasu ayyukan na musamman a fannonin da suka hada da zane-zane da fasahar yara.
 
 

4013070

 

captcha