Mayakan kungiyar ISWAP sun yiwa sojojin Najeriya kwantan bauna a garin Bulguma dake kusa da Askira Uba a Jihar Borno inda suka kashe wasu daga cikin su, ciki har da kwamandan su mai rike da mukamin Birgediya Janar.
Gidan Rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, tawagar motocin sojojin runduna ta 28 ta tashi ne daga Chibok domin kai dauki ga abokan aikin su a Askira lokacin da aka yi musu kwantar bauna akan hanyar su, aka kuma bude musu wuta.
Majiyar sojin ta bayyana alhini kana bin da ya faru da dakarun da suke bakin daga, musamman kisan wasu daga cikinsu da aka yi, da suka hada da babban kwamandansu.
Rahotanni sun ce daga bisani jiragen yakin sojin sun yi ruwan wuta akan mayakan, amma kuma babu cikakken bayani kan abin da yafu na asarorin da ‘yan ta’addan suka yi.
Najeriya dai na daga cikin kasashen yammacin Afirka da suke fuskantar matsaloli na tsaro daga bangarori daban-daban, inda a baya matsalar Boko Haram ce tafi daukar hankula, amma a halin yanzu matsalolin tsaron sun karu musamman aarewacin kasar, da suka hada da na ‘yan ta’adda masu satar mutane da garkuwa da su, da kuma kisan jama’a a kauyuka da satar dukiyoyi gami da shanun jama’a.