IQNA

Zanga-Zangar Wasu Amurkawa Kan Rawar Da Facebook Ke Takawa Wajen Yada Kin Jinin Musulunci

21:24 - November 15, 2021
Lambar Labari: 3486562
Tehran (IQNA) Daruruwan Amurkawa ne suka gudanar da zanga-zanga a birane daban-daban na kasar don nuna adawa da rawar da Facebook ke takawa wajen yada kyamar Musulunci.

Daruruwan mutane ne fadin Amurka suka yi zanga-zangar nuna adawa da rawar da Facebook ke takawa wajen rura wutar kyamar musulmi da kuma cin zarafin mabiya addinin musulunci da 'yan addinin Hindu ke yi a India.
 
Daruruwan mabiya addinai daban-daban ne suka taru a manyan biranen Amurka guda takwas a ranakun Asabar da Lahadi don nuna adawa da shafin Facebook, inda suke zargin kamfanin da ba da damar yada kalaman kyamar musulmi musamman a Indiya, lamarin da ya kai ga cin zarafi, kai hare-hare da kuma kashe mabiya addinai marasa rinjaye da 'yan addinin Hindu ke yi.
 

4013557

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha