IQNA

Ra'isi A Tattaunawarsa Da Putin:

Iran Da Gaske Take Yi Kan Wajabcin Dauke Mata Takunkumai A Matsayin Sharadin Tattaunawar Nukiliya

23:54 - November 16, 2021
Lambar Labari: 3486567
Tehran (IQNA) shugaban kasar Iran Ibrahim Ra'isi ya sheda cewa, kasarsa a da gaske take yi kan wajabcin janye mata takunkumai a matsayin sharadin tattaunawar nukiliya.

Shugaban kasar Iran Ebrahim Ra’isi ya ce Jamhuriyar Musulunci za ta yi iya kokarinta na ganin an dage mata da duk wasu takunkuman da Amurka ta kakaba mata a tattaunawar da za a yi nan gaba a birnin Vienna.
 
A wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a ranar Talata, Ra’isi ya yaba da matsayin Moscow wajen kare yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, da wajibcin kawar da dukkanin takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran, bayan ficewar Washington daga yarjejeniyar ta bai daya.
 
A yayin tattaunawar ta wayar tarho, Putin, shi ma ya jaddada goyon bayan Moscow ga al'ummar Iran kan 'yancin mallakar fasahohin nukiliya tare da bayyana fatan mahalarta taron na Vienna za su sami ra'ayin siyasa da ya dace don kawo karshen takaddamar da ke tattare da yarjejeniyar nukiliyar.
 
A ranar 29 ga watan Nuwamba ne ake sa ran wakilan Iran da sauran bangarorin da suka rage a yarjejeniyar nukiliyar, za su koma bakin tattaunawar neman farfado da yarjejeniyar ta 2015.
 
Tattaunawar mai zuwa idan ta wakana ita ce ta bakwai tsaknanin bangarorin, amma ta farko a karkashin gwamnatin shugaba Ibrahim Ra’asi da aka rantsar a watan Agusta da ya gabata..
 
Kuma tun daga lokacin ne dai sabuwar gwamnatin ta Iran ke yin bitar bayanan da suka shafi jerin tattaunawa guda shida da aka yi a karkashin gwamnatin da ta gabata.
 

4013781

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tattaunawa
captcha