IQNA

Ikirari Kan Ayyukan Ta'addanci Daga Bakin Mataimakin Abubakar Al-Baghdadi

22:48 - November 17, 2021
Lambar Labari: 3486573
Tehran (IQNA) Kafofin yada labaran Iraki sun bayar da rahotanni akan ikirari da mataimakin Abu Bakr al-Baghdadi ya yi bayan kame shi.

Jaridar Qada ta kasar Iraki ta bayar da rahoton cewa, Mataimakin Abu Bakr al-Baghdadi, Haji Hamed, wanda aka kama a wani aikin na musamman da jami'an leken asirin kasar Iraki suka yi a wajen kasar, ya bayyana irin rawar da ya taka a kungiyar ta'addanci ta Da'ish a shekarun baya-bayan nan.

Haji Hamed a cikin ikirari nasa ya bayyana cewa tun bayan faduwar kungiyar ISIS ya yi balaguro tsakanin kasashen turai da dama, amma hukumar leken asirin Iraki ta samu nasarar cafke shi a wani gagarumin samame da aka kwashe watanni shidda ana yi.
 
Hamed, wanda ainahin sunansa shi ne "Sami al-Jubouri" wanda akewa lakabi da "Abu Asia", ya amince cewa shi ne ministan kudi na kungiyar ta'addanci ta Daesh.
 
Ya bayyana cewa al-Baghdadi ya samu gagarumin taimako daga wajensa wajen kashe Abu Ali al-Anbari a watan Maris din shekarar 2016.
 
Haji Hamed dan shekaru 47 da haifuwa ya bayyana cewa ya rike mukamai da dama a kungiyar ta ISIS kuma ya shiga kungiyar Tawhid da Jihad karkashin jagorancin Musab al-Zarqawi a shekara ta 2004.

Rahoton ya kara da cewa: A cewar Hamed, an yankewa Abu Bakr al-Baghdadi hukuncin kisa a shekara ta 2013 saboda ya bayyana alakarsa da shugaban kungiyar Jabhat al-Nusra Abu Muhammad al-Jobani, amma an yi masa afuwa ta hanyar shiga tsakani na kwamandojin ISIS na Iraqi.

Ya ce mamayar da kungiyar ta'adda ta ISIS ta yi a Mosul a shekarar 2014 ya sa Hamed ke karbar makudan kudade a duk wata daga hannun 'yan kasuwar yankin.

4014098

 

 

 

captcha