IQNA

21:14 - November 29, 2021
Lambar Labari: 3486622
Tehran (IQNA) Wasu masu tsattsauran ra'ayi sun kai hari a Masallacin Imam Ali (AS) da ke Pontagros, kuma sun kona kur'ani mai tsarki tare da lalata bangon masallacin.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, kwamitin masallacin ya sanar a safiyar yau cewa; “Muna bakin cikin sanar da ‘yan uwa musulmi cewa wasu mutane ne suka kai wa masallacinmu ba tare da wani dalili ba.

Kwamitin masallacin ya kara da cewa: “Wannan danyen aikin ba wai kawai ya saba wa addinin Musulunci ba ne, har ma da dukkan sauran addinai; Domin a wannan harin an tozarta kalmar masallaci wurin bautar Allah.

Shafin yanar gizo na Brazil (arede) ya bayyana cewa, wadanda suka aikata laifin sun shiga masallacin ne ta hanyar karya kofarsa

Bayanin ya kara da cewa: Baya ga kona kwafin kur’ani mai tsarki, sun kona wani allo da yake rataye da aka rubuta kalmomin Musulunci a kai.

Maharan sun yayyaga litatfai da ke cikin masallacin tare da rusa katangar masallacin, amma babu wani abu da aka sace a cikin masallacin.

 

4016970

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: