IQNA

19:21 - December 02, 2021
Lambar Labari: 3486633
Tehran (IQNA) Dubban 'yan daika ne suka gudanar da taron maulidin Imam (AS) jikan manzon Allah (SAW) a birnin Alkahira na kasar Masar.

Shafin Kinanah News ya bayar da rahoton cewa, a duk shekara a kasar Masar a cikin makon karshe na watan Rabi'ul Thani, mabiya darikun Sufaye na gudanar da gagarumin biki na tunawa da Maulidin Imam Husaini (a.s) a Masallacin Imam Husaini da ke birnin Alkahira.

Mutanen Masar na gudanar da bukukuwan maulidin Imam Husaini sau biyu a shekara, na farko a makon karshe na watan Rabi'ul Thani, na biyu kuma a ranar uku ga watan Sha'aban.

A yayin da kasashen duniya da dama ke shirin gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekara, birnin Alkahira na cike da haske a lokacin maulidin Imam Husaini (AS).

Matsanancin sanyin da ake fama da shi a birnin Alkahira na bana bai  hana dimbin masoya Ahlulbaiti halartar wannan bikin ba, inda suke murna da farin ciki, da karatun kasidu da wakokin yabon manzon Allah (SAW) da Ahlul bait amincin Allah ya tabbata a gare su.

Malaman babbar cibiyar ilimi ta Al-Azhar da Shehunan Sufaye ma suna daga cikin mahalarta wurin, inda ake gabatar da jawabai da kuma kadu na yabon manzon Allah da ahlul bait.

مراسم بزرگداشت ولادت امام حسین (ع) در قاهره (گزارش تصویری)

مراسم بزرگداشت ولادت امام حسین (ع) در قاهره (گزارش تصویری)

مراسم بزرگداشت ولادت امام حسین (ع) در قاهره (گزارش تصویری)

4017852

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: