IQNA

Bisa Matsin Lambar Saudiyya Ministan Yada Labaran Lebanon Ya Yi Murabus

22:26 - December 03, 2021
Lambar Labari: 3486637
Tehran (IQNA) ministan yada labaran kasar Lebanon ya yi murabus daga kan mukaminsa sakamakon matsin lambar gwamnatin Saudiyya.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a cikin jawabin da ya gabatar a yau Juma'a a birnin Beirut a gaban manema labarai, ministan yada labaran kasar Lebanon George Kardahi ya bayyana cewa, "Ban yarda na zama sanadin cutarwa ga Labanon da kuma zalunci a kan 'yan uwana na Lebanon a cikin kasashen yankin tekun fasha ba, saboda Labanon ta fi muhimmanci a gare ni, don haka na yanke shawarar "zan bar mukamina a cikin gwamnatin Lebanon."

Ya kara da cewa: “Babu bukatar a sake maimaita labarin tare da tunatar da cewa an yi ganawar ne kafin nada ni minista, inda a ciki ne na bayyana ra'ayina kan yakin kasar Yemen.
 
Ministan yada labaran kasar Lebanon mai murabus ya yi ishara da yarfen da wasu kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta na Lebanon da kuma kasashen yankin Gulf na Farisa suka yi ta yi masa da gangan, inda ya ce: A saboda wannan yarfen ne aka fara gabatar da bukatu na in yi murabus da kuma kakabawa Labanon takunkumin da kasashen larabawan tekun Farisa."
 
A hirar da ya yi da tashar aljadid ta kasar Lebanon a cikin watan Agustan da ya gabata kafin ya zama ministan yada labarai na kasar, Kardahi ya bayyana yakin da Saudiyya take kaddamarwa kan al'ummar kasar Yemen da cewa aiki ne na wauta, kuma dole ne  akawo karshensa, domin ba shi da wani amfani, kasar larabawa tana yakar 'yan uwanta larabawa.
 
A kan wannan furuci ne masarautar Saudiyya ta tayar da kayar baya daga bisani, bayan da Kardahi ya zama ministan yada labaran Lebanon, inda ta tilasta gwamnatin Lebanon a kan ya yi murabus, da farko dai Kardahi ya yi watsi da hakan, amma sdaga baya ya yanke shawarar ajiye aikin nasa, inda ya ce kasantuwarsa a  cikin gwamnatin Lebanon ba shi da wani alfannu.
Haka nan kuma ya sake jaddada matsayarsa kan cewa abin da Saudiyya take yi na yaki a kan al'ummar kasar Yemen ba shi da wani amfani, kuma dole ne ta kawo karshen hakan.
 
 

4018098

 

 

captcha