A rahoton da shafin mujallar Hill ya bayar, a yau Asabar Ilhan Omar, ‘yar majalisa musulma, za ta samu lambar yabo a wani buki da kungiyar musulmin Amurka ta shirya tare da karrama ta a matsayin babbar Musulma mai hidima a kasar ta Amurka.
A cikin wani faifan bidiyo wanda aka yi ta yin Allah wadai da shi, Bobert ya yi izgili da cewa Ilhan Omar 'yar ta'adda ce, Kalaman da suka haifar da cece-kuce kan lamarin.
Shugabannin jam'iyyar Democrat a majalisar wakilan Amurka sun fitar da wata sanarwa inda suka bukaci Bobert da ya janye kalaman nasa, kuma ya guji maimaita irinsu.
Cibiyar ta CAIR ta fitar da wata sanarwa a makon da ya gabata inda ta kira kalaman Bobert a matsayin abin kyama tare da yin kira ga Majalisa da ta yi Allah wadai da dan majalisar, amma har yanzu Majalisar wakilan Amurka ba ta dauki matakin yin Allah wadai da Bubert ba.