tehran (IQNA) Harris Jay, wani mawaki musulmi dan kasar Birtaniya da ke gudanar da aikin Umrah a kasar Saudiyya, ya saka wani hoton bidiyo nasa yana karatun Alkur'ani a masallacin Annabi a shafukan sada zumunta.

Harris Jay, wanda ainahin sunansa Harris Jung, ya fitar da faifan bidiyo na karatun kur’ani a masallacin Annabi, da kuma hotunan ziyararsa a Masallacin Harami.
Mawakin Chelsea mai shekaru 25 da haihuwa daga Landan, dan asalin Indiya haifaffen Ireland, ya bayyana lokutan da yake kusa da Masallacin Annabi da cewa shi ne lokaci mafi daukaka a cikin lokutansa na rayuwa., ya ce ... na gode wa Allah."
Bidiyon ya sami yabo daga dubban masu bayyana ra'ayoyinsu, kuma an yada shi sosai a shafukan sada zumunta.



