IQNA

Za A Bude Ofishin Cibiyar Radiyo Da Talabijin Ta Musulunci Ta Duniya

23:03 - December 06, 2021
Lambar Labari: 3486650
Tehran (IQNA) Shugaban kungiyar hadin kan gidajen radiyon Musulunci ya bayyana cewa kungiyar za ta bude ofishinta a Falastinu.

hugaban kungiyar hadin kan gidajen radiyon Musulunci Omar Al-Laithi ya bayyana cewa kungiyar za ta bude ofishinta a Falastinu.

Ya ce "Za mu shirya wasu shirye-shiryen da za a watsa a tashoshi 57 na Larabci da na Musulunci cikin harsuna daban-daban," in ji Al-Laithi a yayin bikin ranar hadin kai da nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinu da ke gudana a gidajen talabijin na Masar, Falasdinu, Iraki da Jordan. 
 
Ya kara da cewa: An kafa wannan kungiyar ne a shekara ta 1975 musamman domin kare al'ummar Palastinu da kuma tallafa musu, kuma ita ce babbar kungiyar yada labarai a duniya, wadda ta kunshi kasashe 57.
 
An kafa kungiyar gidajen radiyon kasashen musulmi da larabawa ne a shekara ta 1975 domin cimma manufofin kungiyar hadin kan musulmi tare da amincewar mahalarta taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmi karo na shida.

Kungiyar dai tana da hedikwata ne a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, kuma tana da wakilai a kasashe mambobin kungiyar.

 

4018507

 

captcha