IQNA

Wani Malamin Yahudawa: Isra'ila Ba Ta Da Halasci A Bisa Koyarwar Addinin Yahudanci

20:13 - December 07, 2021
Lambar Labari: 3486654
Tehran (IQNA) wani malamin yahudawa ya ce yadda aka kafa gwamnatin Isra'ila a mahangar addinin Yahudanci haramun ne, kuma dole a mayar wa Falastinawa yankunansu da aka mamaye bisa zalunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Akwai Yahudawa da dama a duniya da ke adawa da mamayar da Isra'ila take yi wa yankunan Falastinawa, inda suke ganin ta keta hurumi da kuma hakkoki na al'ummar Falastinu.

Kungiyar Neturei Karta International na daya daga cikin wadannan kungiyoyin yahudawan da suka kwashe shekaru suna bayyana goyon bayansu ga Palasdinawa da ake zalunta.

a wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labaran iqna, Rabbi Dovid Feldman, mai magana da yawun kungiyar Neturei Karta International, ya ce akwai mutane da dama da ke goyon bayan Falasdinu a zuciya amma ba sa son yin magana a kai saboda ba sa son a zarge su da kyamar Yahudawa.
خاخام ضد اسرائیلی: رژیم صهیونیستی بر اساس قوانین دین یهود غیرقانونی است
 
Ya ce a halin yanzu babban abin da kungiyarsu ta yahudawa masu adawa da Isra'ila suke yi shi ne, suna kokarin wayar da kan al'ummomin duniya kan cewa, kafa Isra'ila ya saba wa addinin yahudanci, musamamn ma kuma yadda aka kafa ta bisa zakunci da kwace yankunan Falastinawa, da zubar da jininsu, da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki na musulmi da kiristoci.
 
Malamin yahudawan ya kara da cewa, suna gudanar da ayyuka daban-daban domin cimma wannan manufa, kuma abin da suke yi yana samun karbuwa a wajen mutane masu lamiri a duniya, da suka hada da yahudawa da ma wadanda ba yahudawa.
 
 

4018876

 

 
 
 
 
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha