IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allawadai Da Harin Ta'addanci A Birnin Basra Na Iraki

23:23 - December 08, 2021
Lambar Labari: 3486661
Tehran (IQNA) Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Iraki UNAMI ta yi Allah-wadai da harin ta'addancin da aka kai a lardin Basra, tana mai cewa wani yunkuri ne na hargitsa kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iraki ya habarta cewa, tawagar ta bayyana cewa: "Muna matukar yin Allah wadai da harin bam na ta'addanci a birnin Basra, muna mika ta'aziyyarmu ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya da kuma samun sauki cikin gaggawa." .
 
Ta ci gaba da cewa hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika, da kuma karfafa hadin kan kasa shi ne zai kawo cikas ga wannan yunkuri na neman  kawo rudani a Iraki.
 
Da alama kungiyoyin 'yan ta'adda daban-daban da suka koma suna gudanar da ayyukansu a asirce  bayan fatattakarsu da dakarun Iraki suka yi a baya-bayan nan sun fara fadada ayyukansu tare da shirya hare-hare da dama a nan gaba.
 
Halin da ake ciki na rashin tabbas ta fuskar siyasa a kasar Iraki, kasancewar sojojin mamaya na Amurka na ci gaba da wanzuwa a kasar, da kuma tasirin nasarorin da aka samu a kan 'yan ta'adda a kasar Siriya, da kuma shigo da wasu daga cikin 'yan ta'adda da suka tarwatse a Syria zuwa kasar Iraki, na daga cikin abubuwan da suke yi tasiri wajen sake dawowar irin wadannan ayyuka na ta'addanci a  kasar.
 
 

 

4019293

 

 

 
 
captcha