IQNA

An Bukaci A Gudanar da Bincike kan kona Kur'ani A Jami'ar Arizona A Amurka

20:24 - December 11, 2021
Lambar Labari: 3486670
Tehran (IQNA) Majalisar musulmin Amurka, a yayin da take yin Allah wadai da wulakanta kur'ani mai tsarki da nassosin addinin muslunci a jami'ar Arizona, ta zargi jami'an Amurka da ta'azzarar kyamar Musulunci a kasar.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, babbar kungiyar kare hakkin bil'adama ta musulmi a Amurka, Council on American-Islamic Relation (CAIR), ta yi kira ga jami'an tsaro na tarayya da na kananan hukumomi da su gudanar da bincike kan kona kur'ani mai tsarki da wasu kayan addinin Musulunci a cikin dakin Jami'ar Arizona.

Kungiyar Dalibai Musulmi na Jami’ar Jihar Arizona a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin Instagram, ta ce an yi wannan wulakanci da zagon kasa a ranar 8 ga watan Disamba a bangaren tattaunawa tsakanin addinai da ke dakin karatu na Hayden; Inda dalibai musulmi da dama ke halarta.

Sanarwar ta ce an kona kwafin kur’ani mai tsarki da kuma littattafan adabin addinin muslunci yana a matsayin tozarci ne ga dukkanin msuulmi na Amurka da ma na duniya baki daya.

 

4019942

 

Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha