IQNA

Kungiyar Jihadul Islami Ta Yi Tir Da Ziyarar Firayi Ministan Isra'ila A Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa

19:16 - December 13, 2021
Lambar Labari: 3486679
Tehran (IQNA) kungiyar Jihadul Islami ta yi Allawadai da kakkausar murya kan ziyarar da firayi ministan gwamatin yahudawan Isra'ila ya kai yau a kasar Hadaddiyar daular Larabawa.

Shafin Falstine Alyaum ya bayar da rahoton cewa, kungiyar Jihadul Islami ta byayana ziyarar da firayi ministan gwamatin yahudawan Isra'ila ya kai yau a kasar Hadaddiyar daular Larabawa da cewa abin  Allawadai ne ga duk wasu masu lamiri a cikin larabawa da musulmi.

Bayanin ya ce, yadda mahukuntan kasar kasar Hadaddiyar daular Larabawa suka fito suka yi wa Firayi ministan Isra'ila tarbe da lalae marhabin a cikin kasarsu, hakan yana nuni da amincewa da abin da Isra'ila take tafkawa na kisan kiyashi a kan al'ummar Falastinu, tare ad halasta mata a hakan a hukuamnce.

Jakadan Isra'ila a Hadaddiyar Daular Larabawa ya bayyana cewa, firaministan Isra'ila Naftali Bennett, zai tattauna batun Iran da kuma batutuwan da suka shafi Isra’ila da UAE, a wata ganawarsa da yarima mai jiran gado na Abu Dhabi, Mohammed bin Zayed, a yau Litinin.

Amir Hayek, jakadan Isra'ila a Abu Dhabi ya ce, a ganawar Bennett da bin Zayed, "Ina ganin ba zai zama sirri ba kan cewa lalle za a tattauna kan batun Iran.

Hayek ya ki yin cikakken bayani game da abin da za a tattauna kan Iran a ziyarar firayi ministan Isra’ila a UAE, amma ya ce baya ga batun Iran din akwai wasu batutuwan da suke da muhimmanci da suka shafi alaka tsakanin bangarorin biyu, kamar yadda ya shaida wa gidan rediyon  Isra'ila a wata hira a yau.

Ita ma jaridar  Isra’ila"Isra'ila Hayom", ta nakalto wasu jami'ai da ba a bayyana sunayensu ba, da suke cewa tabbas shugabannin na Hadaddiyar daular larabawa da Isra’ila, za su tattauna batun makaman Iran, da kuma jiragen yaki marasa matuki da take kierawa, wadada take bai wa wasu bangarori a cikin yankin gabas ta tsakiya  a cewarsu.

 

4020481

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha