IQNA

Kudurin Dokar Yaki Da Kyamar Musulunci Ya Haifar Da Cece-Kuce A Majalisar Dokokin Amurka

15:38 - December 15, 2021
Lambar Labari: 3486686
Tehran (IQNA) An gudanar da zaman tattauna daftarin kudirin dokar yaki da kyamar musulunci a majalisar wakilan Amurka, wanda ‘yar majalisa Ilhan Omar ta gabatar.

Jaridar Quds Al-arabi da ake bugawa a Landan ta bayar da rahoton cewa, Majalisar wakilan Amurka ta yi nazari kan kudirin dokar yaki da kyamar Musulunci, tare da neman bude ofishi na musamman a ma’aikatar harkokin wajen Amurkan domin yaki da kyamar musulmi, sakamakon yadda wani dan majalisa daga jam’iyyar Republican ya yi cin zarafi da tozarci a kan addinin muslunci a cikin majalisar.

Scott Perry, dan jam’iyyar Republican, ya kira Ilhan Omar musulma ‘yar majalisar wakilai da ta gabatar da kudirin,  da cewa mai kyamar Yahudawa ce, kuma tana da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

A makonnin da suka gabata, Lauren Pobert, wadda ita ma wata ‘yar majalisar wakilan Amurka ce, ta yi kalaman wariyar launin fata da kuma tozarci ga Ilhan Omar saboda kasantuwarta musulma, inda ta ce Ilhan Omar na iya zama ‘yar ta’adda ko kuma ‘yar kunar bakin wake.

‘Yan jam’iyyar Democrat a majalisar wakilan kasar Amurka sun nuna bacin ransu matuka  bayan kalaman batanci ga Ilhan Omar, yayin das hi kuma Scott Perry ya yi ikirarin cewa an rubuta daftarin kudirin dokar da Ilhan Omar ta gabatar ne tare da hadin baki da  jam’iyyar Democrat, domin hana sukar ayyuan ta’addanci.

A karshe dai an dakatar da muhawarar da ake yi a majalisar dokokin Amurka bayan da 'yan jam'iyyar Democrat suka nuna rashin gamsuwa da kalaman Perry, tare da neman ya janye dukkanin maganganun da ya yi, na batuncin ga Ilhan Omar da kuma jam’iyyar democrat.

 

4021060

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha