IQNA

Taliban: Dole Amurka Ta Biya Diyyar Wadanda Ta Kashe A Harin Da Ta Kai A Kabul

20:04 - December 16, 2021
Lambar Labari: 3486693
Tehran (IQNA) Taliban tace dole ne Amurka ta biya diyyar mutanen da ta kashe a harin da ta kai a birnin Kabul da jirgi maras matuki.

Kakakin Taliban ya ce sojojin Amurka ne ke da alhakin kashe fararen hular Afganistan ta hanyar hare-haren jiragen sama marasa matuka, kuma ya kamata gwamnatin Amurka ta biya iyalan wadanda harin ya rutsa da su.

Zabihullah Mujahid, kakakin Taliban ya ce "Muna son taimakawa iyalan wadanda aka kashe a Afganistan." Dole ne Amurka ta biya diyya, wannan shi ne fatan al'ummar Afghanistan, amma Amurkawa sun ki amincewa da hakan.

Ya kara da cewa: Amurka ta yi irin wadannan abubuwa da dama a duniya, kuma a yanzu ta ce ba za a hukunta sojojinta wadanda ke da hannu a kisan fararen hula ta hanyarkai hare-hare ba.

Amurka ta kashe mutanen da dama wadanda ba su ji ba su gani ba a Afghanistan cikin shekaru 20 da suka gabata, saboda haka wannan wajibi ne kan Amurka ta biya diyyar mutanen da ta kashe a wannan kasa.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta fitar a jiya ta ce, babu wani soja da za a hukunta kan harin da jirgin yakin Amurka ya kai kuma ya kashe fararen hula 10 da suka hada da yara 7 a birnin Kabul babban birnin kasar Afganistan a watan Agustan da ya gabata.

A cewar rahoton, ma'aikatar tsaron Amurka ta amince a cikin watan Satumba cewa harin da jiragen yakin Amurka suka kai a kwanaki na karshe na janyewar da Amurka ta yi daga Afganistan wani mummunan kuskure ne da ya shafi fararen hula.

4021213

 

captcha