IQNA

A karon Farko An Gudanar Da Babban taro Na Shugabannin Musulmi Na Kasar Ghana

18:09 - December 17, 2021
Lambar Labari: 3486694
Tehran (IQNA) A jiya 16 ga watan Disamba ne aka kammala taron farko na shugabannin addinin Islama na kasar Ghana, wanda aka gudanar da nufin kusanto da kungiyoyin addinin musulunci a kasar.

A karon Farko An Gudanar Da Babban taro Na Shugabannin Musulmi Na Kasar Ghana

Shafin Joy Online ya bayar da rahoton cewa, Taron na kwanaki uku ya mayar da hankali ne kan rawar da shugabannin addinin Musulunci ke takawa wajen ci gaban kasar, inda aka dora wa limamai da shugabanin musulmi aikin samar da tsari da wanda zai taimaka wajen samar da fahimtar juna tsakanin dukkanin musulmin kasar.

 
Sheikh Mustafa Ibrahim, wakilin Sheikh Othman Nuhu Sharbato, shugaban musulman kasar Ghana, ya bayyana a wurin rufe taron cewa, samuwar irin wadannan tsare-tsare zai kawo karshen rudani da rikici a tsakanin musulmi idan ya zama dole a maye gurbin shugaba a dukkanin mazhabobin Musulunci.
 
Ibrahim wanda shi ma ya jagoranci bikin rufe taron, ya jaddada cewa, bai kamata a jira shugaban musulmi na wani yanki ko kasa ya mutu ba, don sanin wanda zai gaje shi, amma ana iya yin hakan a lokacin rayuwarsa domin kaucewa wasu matsaloli.
 
Dukkanin shugabannin addinin musulunci 16 daga sassa daban-daban na Ghana, da wata tawaga daga ofishin jagoran musulman Ghana da wasu limamai daga masallatai daban-daban na Ghana sun halarci taron.
 
An gudanar da taron ne a garin Sunyani na kasar Ghana.
 
 

 

4021439

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar Ghana ، halarci ، musulman Gahan ، sassa daban-daban ، tawaga ، mazhabobi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha