IQNA

Amir Abdullahian ya jaddada goyon bayan Iran ga al'ummar Palastinu da 'yantar da birnin Kudus

22:17 - December 19, 2021
Lambar Labari: 3486705
Tehran (IQNA) A zantawarsa da takwaransa na Palasdinawa, ministan harkokin wajen Iran ya jaddada goyon bayan kasarsa ga al'ummar Palastinu da 'yantar da birnin Qudus, tare da yin Allah wadai da ci gaba da aikata laifuffukan da yahudawan sahyoniya suke yi a yankunan da ta mamaye.
A ganawar da ministan harkokin wajen kasar Iran Hussein Amir Abdullahian da ministan harkokin wajen Palasdinu suka yi, a gefen taron ministocin harkokin wajen kungiyar OIC, ministan harkokin wajen na Iran  ya jaddada goyon bayan kasarsa ga al'ummar Palastinu da 'yantar da Qudus mai tsarki, tare da yin kira da a hukunta yahudawan sahyuniya masu tafka laifukan yaki a cikin yankunan Falastinawa da suka mamaye.
 
A gefen taron, ministan harkokin wajen Iran ya gana da ministocin harkokin wajen kasashen Jordan, Turkiyya, Jamhuriyar Azarbaijan, Saliyo da sabon babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi.
 
Amir Abdullahian, a wata ganawa da Hussein Ibrahim Taha, sabon babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi, ya taya shi murnar nadin da aka yi masa, tare da jaddada muhimmancin rawar da kungiyar OIC da babban sakataren kungiyar za su iya takawa wajen taimakawa wajen magance matsaloli da rikice-rikice a cikin al’umma, da duniyar musulmi ciki har da Afghanistan da Falasdinu.
 
A safiyar yau Lahadi 19 ga watan Disamba ne aka fara taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen musulmi karo na 17 a birnin Islamabad na kasar Pakistan.
 
 
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha