IQNA

An Kunna Fitilun Bishiyar Kirsimeti A Kyrgyzstan

14:41 - December 20, 2021
Lambar Labari: 3486706
Tehran (IQNA) An fitar da faifan bidiyo na wata bishiyar Kirsimeti da ake kunnawa a Bishkek, babban birnin kasar Kyrgyzstan, a jajibirin haihuwar Annabi Isa (AS)

A yayin wani biki a Bishkek, babban birnin kasar Kyrgyzstan, an kunna babbar bishiyar Kirsimeti ta kasar.

An ce karamar hukumar Bishkek ta kashe som (kudin Kyrgyz) miliyan 5.7 don kawata bishiyar sabuwar shekara da dandalin Alato (inda aka nuna bishiyar).

Bishiyar Kirsimeti dai ado ne, kuma yawanci bishiyar ana kayata ne da fitilo masu haskaklawa da ke nuni da murna da farin ciki.

Haka nan kuma suna sanya taurari da aka yi da wasu abubuwa masu kyalli a kan bishiyar, wanda duka al'adu ne da mabiya addinin kirista suke yia  irin wannan lokaci a ko'ina cikin fadin duniya.

 

4022020

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: fadin duniya ، addinin kirista ، bishiya ، kirsimeti ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha