IQNA

Allah Ya Yi Wa Sheikh Ali Naklawi Daya Daga Cikin Malaman Kur'ani A Masar Ya Rasu

16:09 - December 22, 2021
Lambar Labari: 3486714
Tehran (IQNA) Kafofin yada labaran kasar Masar sun ba da rahoton rasuwar Sheikh "Rafiq Ali Al-Naklawi", shahararren malamin addinin musulunci na kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Masar Al-Akhbar Al-Youm ya bayar da rahoton cewa, Sheikh Rafiq Ali al-Naklawi ya rasu a safiyar yau Laraba 22 ga watan Disamba, kuma an shirya yi jana'izarsa a garinsa na lardin Al-Bahira.

A cewar shafin na Masar, Sheikh Rafiq Ali al-Naklawi ya fara shiga gidan rediyon Masar yana da shekaru 40 a duniya domin gudanar da wa'azi da fadakarwa.

Tun yana karami ya kasance yana sha’awar rera baitocin yabon Manzon Allah (SAW) da halartar taruka  Ibtihal.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Yawm News cewa, an buga wani bangare na bayanin Al-Naklawi a wata hira da ya yi da kafafen yada labarai, inda ya yi bayani kan wasu muhimman lamurra da suka shafi rayuwarsa.

 
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4022755
Abubuwan Da Ya Shafa: babban malamin addini ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha