IQNA

Wasu Yahudawa Sun Kutsa Kai Cikin Masallacin Quds Sanye Da Kayan Musulmi

21:02 - December 22, 2021
Lambar Labari: 3486715
Tehran (IQNA) Sheikh Ikrima Sabri, babban limamin masallacin Al-Aqsa, ya yi gargadi kan sabbin hanyoyin kutsa kai cikin masallacin Al-Aqsa da yahudawa suke dauka.

Wata kafar yada labaran yahudanci ta bayar da rahoton cewa, wasu gungun yahudawan sahyoniya sanye da rigar addinin muslunci, suna kutsa kai cikin cikin masallacin Quds, tare da gudanar da bukukuwan Talmud yahudawa cikin walwala a wurin ibadar na musulmi.

Dangane da haka, Sheikh Ikrima Sabri, yayin da yake yin gargadi game da ayyukan tunzura 'yan sahayoniyawan ya ce: Manufar yahudawan sahyoniyawan ita ce su yaudari masu gadin masallacin Aqsa domin kada su gane kamanninsu, ya ce Duk da haka masu gadin sun gane da yawa daga cikin yahudawan a lokacin da su ke kokarin shiga masallacin Al-Aqsa.

Ya kara da cewa: Sanya tufafin Musulunci da yahudawan sahyoniya suke yi yana nuni da irin hadarin da da masallacin Aqsa ke fuskanta daga yahudawa 'yan share wuri zauna, Don haka ya zama wajibi masu gadin masallacin da masallata musulmi su sanya ido wajen zakulo wadannan ’yan ta’adda.

Yayin da yake ishara da irin rawar da ofishin bayar da agajin ya taka dangane da hakan, Sabri ya ce: Matsayin wannan ofishin yana da matukar muhimmanci, kuma ya zama wajibi su dauki nauyin gudanar da ayyukansu, da hana sojojin yahudawan sahyoniya su tsoma baki cikin harkokin masallacin Masallacin Aksa."

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4022849

 

Abubuwan Da Ya Shafa: bayar da agaji ، gudanar da ، masallacin Aqsa ، gargadi ، masu gadi ، musulmi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha