IQNA

Kwamitin Sulhu na MDD ya amince da kai taimakon jin kai a kasar Afghanistan

12:39 - December 24, 2021
Lambar Labari: 3486722
Tehran (IQNA) Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da wani kuduri na bai daya da zai share fagen gudanar da ayyukan jin kai ga kasar Afganistan.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Kudurin ya ba da izinin biyan kudade, samar da kayayyaki da ayyukan da suka dace don biyan bukatun yau da kullun na jin kai a Afghanistan, ba tare da yin la'akari da takunkumin da aka saka wa kungiyoyin da ke da alaka da Taliban ba.

Amurka ta yi marhabin da matakin, kuma jakadanta a kwamitin tsaro ya ce matakan da ba a sanyawa takunkumi ba sun hada da samar da matsuguni ga 'yan kasar Afganistan da kayayyakin masarufi kamar abinci, kiwon lafiya da ilimi.
 
A nasa bangaren, wakilin kasar Sin ya jaddada cewa, bai kamata taimakon jin kai ya kasance cikin sharadi kan harkokin siyasa a kowane irin yanayi ba, ya kuma yi kira da a gaggauta sakin kadarorin kasar Afganistan da ke a kasashen ketare.
 
Shi ma Wakilin Rasha ya bayyana goyon bayansa ga wannan shawarar, yana mai cewa kai taimakon gaggawa ga al'ummar Afghanistan nauyi ne da rataya kan duniya.
 
Bayan amincewa da wannan kudiri na kwamitin sulhu na saukaka kai kayan agaji zuwa Afganistan, kungiyar Taliban ta yi marhabin da matakin, tana mai cewa matakin ci gaba ne, tare da fatan matakin zai  share fage na dage takunkumin.
 
Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa: "Wannan mataki ne mai kyau kuma mun yaba da hakan domin yana iya taimaka wajen inganta yanayin tattalin arzikin Afghanistan."
 
Ya bayyana fatan cewa matakin zai sa a gaggauta dage takunkumin tattalin arziki da aka kakaba wa Taliban.
 
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa; Majalisar Dinkin Duniya ta yi tayin biyan kusan dalar Amurka miliyan 6 domin biyan masu bayar da kariya ga hedikwatarta da ke Afganistan.
 
Za a biya kasafin kudin ne ga ma'aikatar harkokin cikin gida ta Afganistan domin biyan albashin mayakan Taliban da ke gadin hedkwatar kungiyoyin kasa da kasa a kasar.
 
 

 

 

 

 
Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha