IQNA

Jakadan Kasar Jamus A Iraki Ya Ziyarci Hubbaren Imam Hussain (AS) A Karbala

17:47 - December 24, 2021
Lambar Labari: 3486723
Tehran (IQNA) Jakadan Jamus a Iraki ya ziyarci hubbaren Imam Husaini (AS) da kuma dan uwansa Sayyidina Abbas (AS) a Karbala.

Tashar talabijin ta Alkafil ta bayar da rahoton cewa, Martin Yig, sabon jakadan Jamus a kasar Iraki, ya ziyarci haramin Imam Husaini (AS) da kuma Sayyid Abbas (AS) a ranar Laraba 22 ga watan Disamba, inda ya gana da Hojjatoleslam Ahmad Al-Safi, majibincin Astan Abbasi, da Mohammad. Al-Ashiqar, babban sakatare na haramain.

A yayin ganawar, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi kan batutuwa daban-daban, kuma Hojjatoleslam Safi ya yi maraba da jakadan na Jamus, tare da taya shi murnar samun wannan matsayi da kuma yi masa fatan samun nasara.

Ganawar tasu ta mayar da hankali kan wasu ayyuka a hubbaren Abbasi da kamfanonin Jamus ke da hannu a cikinsu, kamar ayyukan madaba'antu, kiwon lafiya da kuma gidajen tarihi, inda a karshen ganawar jakadan na Jamus ya yaba da ayyukan da ake gudanarwa a fannoni daban-daban.

تشرف سفیر المان در عراق به حرم مطهر امام حسین (ع) و حضرت عباس(ع) +عکس
 
تشرف سفیر المان در عراق به حرم مطهر امام حسین (ع) و حضرت عباس(ع) +عکس
 
تشرف سفیر المان در عراق به حرم مطهر امام حسین (ع) و حضرت عباس(ع) +عکس

https://iqna.ir/fa/news/4023112

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha