Tashar russia Today ta bayar da rahoton cewa, A karon farko a tarihin kasar Saudiyya an gudanar da bukukuwan Kirsimeti a kasar, kuma hukumomin kasar sun ba da izinin kafa bishiyar Kirsimeti da kayan ado na musamman.
Jaridar Wall Street Journal ta bayar da rahoton cewa, a wani bangare na manufofin Saudiyya na kawo sauyi a baya-bayan nan, shaguna a Riyadh, babban birnin kasar, sun baje kolin itatuwan pine da bishiyu na wucin gadi da mutane za su iya sanyawa da huluna na Santa Claus, da kuma sayen zane-zane ko kuma barewa da aka sassaka daga itace da sauransu.
Gidaken cin abinci suna bayar da kek na Kirsimeti, musamman mawanda yawanci ana shirya shi a ranar Sabuwar Shekara.