IQNA

Zanen Hotunan Qasem Sulaimani Da Abu Mahdi Muhandis A Filin Saukar Jirage Na Beirut

22:53 - December 26, 2021
Lambar Labari: 3486734
Tehran (IQNA) An saka wani babban allo da ke dauke da zanen Qasem Sulaimani da Abu mahdi Muhandis a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Beiruta Lebanon.

Shafin yada labarai na Al-ahad ya bayar da rahoton cewa, a daidai lokacin da ake tunawa da cikar shekaru biyu da shahadar manyan kwamnadoji biyu na dakarun Iran da Iraki, an saka wani babban allo da ke dauke da zanen Qasem Sulaimani da Abu mahdi Muhandis a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Beiruta Lebanon.

A kwanakin baya ne 'yan kasar Labanon suka fara dasa itatuwa a yankin kudancin kasar da sunan tunawa da Janar Haj Qassem Soleimani.
 
Janar Qassem Soleimani ya yi shahada ne a safiyar ranar Juma'a 1 ga watan Janairun 2020 a wani hari da Amurka ta kai kusa da filin jirgin saman Bagadaza.
 
Harin dai ya yi ajalinsa ne tare da Abu Mahdi al-Mohandes, kwamandan dakarun sa kai na kasar Iraki na lokacin, da wasu daga cikin mayakan Irakin.
 
An kai harin ne bisa umarnin tsohon shugaban Amurka Donald Trump kai tsaye.

 

 

4023678

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha