IQNA

Sheikh Qais: Dole Ne Sojojin Amurka Su Fice Daga Iraki A Lokacin Da Aka Ayyana  Musu

20:59 - December 27, 2021
Lambar Labari: 3486738
Tehran (IQNA) Dakarun Asaeb Ahl al-Haq sunj bukaci sojojin Amurka da su fice daga Iraki zuwa lokacin da aka diba musu.

Sheikh Qais al-Khazali Sakatare Janar na dakarun sa kai na Asaeb Ahl al-Haq a Iraki, yayin da yake ishara da bukatar ficewar sojojin Amurka daga kasar Iraki kan lokaci da kuma sharuddan da aka riga aka ayyana, ya jaddada cewa al’ummar Iraki suna hakkin daukar dukkanin matakin da suka gay a dace matukar dai sojojin na Amurka ba su daga kasarsu ba.

Sakatare Janar Asaeb Ahl al-Haq ya fadi cewa, Amurka ba ta bayar da wata tsayayyar magana ta janyewa daga Irakin ba, yana mai bayyana kalaman da take yi a matsayin na siyasa, sai dai kawai ta sauya sunayen dakarun da ke da su, daga masu yaki zuwa masu bada shawara.

Sheikh Al-Khazali ya kara da cewa: Ficewar tsarin makaman kariya na Patriot daga kasar Iraki ba shi da alaka da yarjejeniyar ficewar da kasar, illa dai ya shafi manufofin Amurka a yankin baki daya.

Ya kara da cewa: Hare-haren na kin amincewa da kasancewar duk wani sojan Amurka a sansanonin Ain al-Assad da Harir, ishara ce kan cewa Irakawa ba za su amince da shawagin duk wani jirgin saman soji ba, hatta jiragen Amurka maras matuki.

Sakatare-Janar Asaeb Ahl al-Haq ya yi watsi da batun jibge sojojin Amurka 2500 a matsayin masu bayar da shawara kan harkokin tsaroa  cikin kasar Iraki, yana mai jaddada cewa adadin masu ba da shawara ya dogara ne da ra'ayin hukumomin tsaro na Iraki, kuma ba za a tantance shi ba bisa bukatar Amurka.

Ya kara da cewa: "Idan sojojin Amurka ba su janye ba bisa sharuddan da aka sanar ba, to su tabbatar da cewa su ne ke da alhakin duk wani mataki da al’ummar Iraki suka dauka a kansu.

 

4023787

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha